Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Ma'aikatar Lafiya ta Lebanon, yayin da take sanar da adadin shahidan hare-haren gwamnatin Sahayoniya a jiya a ƙasar, ta ce daga ranar 11 ga watan Maris zuwa yau, mutane 2,896 ne suka yi shahada, yayin da mutane 8,824 suka jikkata sakamakon hare-haren Sahayoniyawa.
Wakilin Al-Mayadeen ya sanar da cewa adadin farko na harin da Isra’ila taka kai kan motoci biyu a hanyar al-Jiyah a yankin al-Shouf a tsaunin Lebanon, ya kai 4 shahidai. A yayin hare-haren da aka kai a jiya a Beirut da kudancin Lebanon, wasu 'yan ƙasa 9 sun shahada.
Sannan Rakan Nasiruddin, Ministan Lafiya na Lebanon, ya bayyana cewa gwamnatin Sahayoniya tun daga ranar 2 ga Maris zuwa yanzu ta shahadar mutane 108 daga cikin ma'aikatan agaji da likitoci a Lebanon yayin hare-haren da take kai wa ƙasar.
Your Comment